"Yan Ta’adda 200,000 da suka tuba suka ajiye makamansu kuma sun mika wuya ga sojoji a yankin Arewa"_-Inji- Christopher Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kimanin ‘yan ta’adda 200,000 da suka tuba suka ajiye makamansu kuma sun mika wuya ga sojoji a yankin Arewa Maso Gabas. Ya danganta wannan nasara ga dabarun aiki guda biyu, wato na amfani da karfi da kuma dabaru na sulhu.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa kan Tsaro da Adalci wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) tare da hadin gwiwar Jakadancin Birtaniya suka shirya, wanda ya gudana a Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa da ke Abuja, a ranar Talata.
~Karaduwa Post