TIRƘASHI: An Bankaɗo Yadda Aka Ɓoye Shinkafar Da Gwamnatin Tarayya Ta Ke Raba wa Talakawa A Jahar Kano-

 Hukumar karɓan ƙorafe-ƙorafen jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jahar Kano (PCACC) ta yi dirar mikiya a wani ɗakin da aka ɓoye shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar a raba wa jama'a don rage raɗaɗi. 

Hukumar ta gano tarin buhunhunan Shinkafar da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.3 wanda gwamnatin tarayya ta raba mai dauke da tambarin *Ba Ta Sayarwa Ba ce*, jibge inda ake sauya musu buhu domin sayarwa a kasuwannin bayan fage.

Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, ya yi Allah-wadai da wannan al'amari inda ya kira lamarin da wani nau'i na cin hanci da rashawa mara ɗigon tausayi, a lokacin da al'ummar kasar ke cikin mawuyacin hali. 

Hukumar ta kama mutum guda tare da shan alwashin gudanar da kwakkwaran bincike domin bankado ƙarin wadanda ke da hannu a badaƙalar.

Shinkafar da aka kama, wadda ta kai buhu dubu 16,800, na daga cikin tallafin abincin azumin watan Ramadan da ya gabata wanda gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta bayar don rage wa mutanen ƙasar raɗaɗi a lokacin da suke azumtar watan.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org