Yahaya Bello ya musanta zarge-zargen da EFCC ke yi masa
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya musanta zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi masa bayan an gurfanar da shi a kotu a Abuja a yau Laraba.
EFCC ta gurfanar da Bello bisa zargin laifuka 16 da suka hada da karkatar da kudade da su ka kai Naira biliyan 110.
Sauran wadanda ake tuhuma tare da Bello sun hada da Umar Shoaib Oricha da Abdulsalami Hudu, wadanda su ma su ka musanta -tuhumen.
Joseph Daudu, lauyan Bello, sai yd mika rokon bada belin wanda ya ke karewa, amma sai lauyan EFCC Kemi Pinheiro ya soki rokon.
#Daily Nigeria Hausa