A jihar Kano Gwamnatin Kanon Ta Rufe Ofishin Kamfanin Dantata Da Jirgin Max Saboda Zargin Rashin Biyan Haraji

 Hukumar tara haraji ta jihar Kano ta rufe babban ofishin jirgin saman Max Air saboda zargin rashin biyan harajin ma'aikatan kamfanin 


Hukumar tara haraji ta jihar Kano ta rufe babban ofishin jirgin saman Max Air saboda zargin rashin biyan harajin ma'aikatan kamfanin wato PAYE na naira miliyan 190 da sauran na'ukan haraji tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017.

Matakin wani ɓangare ne na yaƙi da marasa biyan haraji a jihar. A cewar ofishin Darakta mai kula da basussuka na KIRS, hukumar ta dauki matakin rufe harabar kamfanin ne bayan da aka yi ƙoƙarin sasanta lamarin ta hanyar tattaunawa.

"Mun aika wasiƙu da dama zuwa ga Max Air don daidaita bashin harajin su, amma ba mu sami amsa daga garesu ba. A matsayin matakin na ƙarshe, mun samu umarnin kotu na rufe hedikwatarsu kamar yadda doka ta tanada,” in ji ofishin.

Kamfanin Max Air, mallakin Dahiru Barau Mangal, fitaccen ɗan kasuwa kuma surukin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa, ba shi ne kaɗai kamfanin da matakan suka shafa ba.

Hukumar KIRS ta kuma rufe ofisoshin kamfanin Dantata and Sawoe da ke kan titin Zaria bisa laifin rashin biyan sama da Naira miliyan 241 na harajin PAYE da sauran haraje-haraje daga 2021 zuwa 2022. Haka kuma ta rufe kamfanin Northern Rice and Oil Milling Nigeria Ltd da ke gudumawa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org