Sarkin Muslim Ya ce "Sarakuna ba sa tsoron gwamnoni"

 Maibartaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya musanta zancen cewa sarakunan gargajiya na jin tsoron gwamnonin jihohi.

Daily Trust ta rawaito cewa Sarkin ya ce sarakunan gargajiya sun fara mulki tun kafin a kafa Najeriya a shekarar 1960, yana mai cewa a matsayin sarakuna, suna da babbar rawar da suke takawa da kuma fahimtar kasa fiye da gwamnonin jihohi.

Ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya.

Sarkin gargajiyan ya kuma mayar da martani kan furucin tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya na jin tsoron gwamnonin jihohinsu.

A cewar Sarkin Musulmi, “Na ji  ana cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. A’a, sarakunan gargajiya ba sa jin tsoron gwamnonin. Sarakuna kawai suna girmama kansu, suna girmama gwamnonin da ke da iko a jihohi daban-daban, ba wai tsoro ba.

“Duk abin da ya faru, ba ma saduda. Muna barin komai ga Allah Madaukakin Sarki, wanda yake kawo sauye-sauye a duniya, kuma muna karɓar sauye-sauyen kamar yadda suka zo.”

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org