Kasheem Shetima ya kira Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16

 A cikin wani sakon fatan alkhairi da ya wallafa a shafinsa na Dandalin X wato Twitter, Mataimakin shugaban kasa Kasheem Shetima ya ce, "A ranar Asabar, na halarci daurin auren ɗiyar tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Kwankwaso".

"Kwankwaso ya aurar da ɗiyar sa Dakta A'ishatu Kwankwaso ga ɗan gidan hamshaƙin ɗan kasuwa na jihar Katsina Alhaji Ɗahiru Mangal."

"Taron ɗaurin auren ya gudana ne a fadar mai martaba sarkin Kano na 16 Alhaji Muhammad Sanusi II, yayin da babban limamin jihar Farfesa Sani Zaharaddeen ya jagoranci daurin auren".

"Ina isar da kyakkyawan fatan alheri ga Ma'auratan, tare da fatan za suyi rayuwar aure cikin aminci da salama."

Sai dai bayan wallafa sakon, ma'abota amfani da kafofin dandalin sada zumunta suna ta tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda mataimakin shugaban kasar ya kira Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16, duk da cewa har yanzu dambarwar Sarautar tana a gaban kotu, kuma ba a kai ga yanke hukunci ba.

Shin ko hakan na nufin Muhammad Sanusi II shine halastaccen Sarkin Kano?


Daga Lukman Aliyu Iyatawa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org