Faransa ta buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin Sudan

 Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya yi kira ga ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna a Sudan su ajiye makamai domin kawo ƙarshen yaƙin da suka daɗe suna gwabzawa.


Mista Barrot na wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyara wani sansanin ƴan gudun hijira da ke Adre a ƙasar Chadi, wanda ke kusa da kan iyakar Sudan.


A game da zargin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da tallafa wa dakarun RSF da makamai, ta hanyar amfani da Chadi a matsayin mahaɗa, ministan harkokin wajen Chadi, Abderaman Koulamallah ya ce babu ruwansu a yaƙin kuma ba sa goyon bayan kowane ɓangare tsakanin sojojin Sudan ɗin da dakarun RSF.


Mista Barrot ya kuma yi kira ga hukumomin Sudan su bar kan iyakar Adre a buɗe domin samun damar shigar da kayayyakin agaji, sannan ya yi kira ga dakarun RSF su guji ƙwacewa tare da karkatar da kayayyakin agajin da aka kawo domin waɗanda suke fuskantar ƙuncin rayuwa a sanadiyar yaƙin.


Ministan ya kuma yi alƙawarin ƙarin fam miliyan bakwai domin taimakon ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya domin yaƙi da kwalara da tallafa wa mata.


Rana24

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org