Da Atiku ne Shugaban ƙasa, da Najeriya sai tafi haka Muni – Onanuga

Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da martani kan tsohon mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar bisa kalaman da ake yi akan sa cewa da ya yi nasarar zama Shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da sai yayi abin azo a gani.
Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga a ranar Lahadi, ya mayar da martani ga kalaman Atiku, inda ya ce da Atiku ya yi nasara da sai ya jefa Najeriya cikin tabarbarewar tattalin arziki fiye da yadda take a yau.

Kun tuna cewa ɗan Takarar Shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku ya fitar da wasu matakai da zai ɗauka domin ceto tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai Onanuga ya zargi Atiku Abubakar da kokarin kushe shirin Shugaba Tinubu na sake fasalin tattalin arziki tare da bayyana manufofinsa a matsayin abinda ya fi zama bisa tsari.

A cewar mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan harkokin yada labarai manufofin Atiku ba su da tsari, kuma ƴan Najeriya ba su amince da su ba shiyasa yasha ƙasa a zaben 2023.

“Idan da ya ci zabe, mun yi imanin da ya jefa Najeriya cikin wani mawuyacin hali ko kuma ya gudanar da Mulkin kama-karya.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org