An Samu Kulla Yarjejeniya Alaka da Gwamnatin Jihar Katsina kan haƙar ma'adinai ta biliyoyin Kudi
Gwamnatin Katsina ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai a faɗin jihar da kamfanin Geoscan na ƙasar Jamus.
Shugaban hukumar haƙar ma'dinai ta jihar Katsina, Umar Abbas Dangi ne ya bayyana haka yayin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tare da wakilan kamfanin Geoscan a Berlin.
Abbas wanda ya wakilci gwamna Dikko Umaru Radda, ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen samarwa jihar kuɗaɗen shiga da kuma ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa ganin kwarewar Geoscan wajen aikin haƙar ma'adinai a Najeriya, ya janyo suka kulla yarjejeniyar.
"Kamfanin ya kware wajen haƙar ma'adinai yadda ya dace ba tare da yin wani mummunan tasiri kan muhalli ba," in ji Umar Dangi.
Sun yaba wa gwamna Radda da wannan yunkuri da ya yi wajen ganin ɗorewa da kuma bunƙasar ɓangaren haƙar ma'adinai.
@BBC HAUSA