An Bayyana Dalilan Da Suka Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Talauci Duk Da Karuwar Kudin Shiga – Masana
Wasu Masana tattalin arziki da kwararru a bangaren hada-hadar kudi a Nijeriya sun yi bayanin dalilan da suke janyo har yanzu al’ummar Nijeriya ke fama da talauci da fatara duk kuwa da cewa a ‘yan watannin da suka gabata tattalin arzikin kasar (GDP) ya karu da kaso 3.46 a zango na uku na shekarar 2024.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da daraktan kididdiga na tarayya, Adeyemi Adeniran Adedeji, ya sanar a ranar Litinin cewa tattalin arzikin Nijeriya ya fadada zuwa da kaso 3.49 a zango na uku na 2024 daga kaso 3.19 a zango na biyu na 2024.
Bangarorin da suka taimaka wajen karuwar tattalin arzikin Nijeriya sun hada da sashin ayyuka, cibiyoyin hada-hadar kudade, kamfanonin sadarwa, noma, sufuri da kuma bangaren gine-gine.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta wata sanarwar da kakakinsa Sunday Dare, ya nuna gayar farin cikinsa kan ci gaban da tattalin arzikin cikin gida ya samu. Inda ya misalta hakan da cewa zai kara kyautata tattalin arziki.
Sai dai kuma duk da karuwar lambobin a bangarorin, wannan lamarin bai nuna wani tasiri ga rayuwar al’ummar Nijeriya ba. A zahirance dai, ‘yan Nijeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, wanda ya kasance kaso 33.87 da kaso 39.1 to6 a watan Oktoba. Hauhawar farashin na ta da wa al’umman kasa hankali da jefa su cikin matsin rayuwa.
@Leadership Hausa