An sace Dala Miliyan 17 daga asusun babban bankin kasar Uganda
Satar dala miliyan 17 daga Babban Bankin Uganda ta jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar kan wanene ya aikata wannan aika-aikar.
A baya, rahoton jaridar New Vision ya bayyana cewa masu satar bayanai sun kutsa cikin tsarin Babban Bankin Uganda suka kuma sace shilingi biliyan 62 (dala miliyan 17) daga asusun bankin.
Rahoton ya ce harin an kai shi ne ta hannun wata kungiya mai suna "Waste," wadda take da mazauni a kudu maso gabashin Asiya, kamar yadda jaridar da ke birnin Kampala ta bayyana ranar Alhamis, tana dogaro da bayanai daga wasu da ba a bayyana sunansu ba.
Sai dai wani rahoto daga jaridar Daily Monitor ya ce shilingi biliyan 47.8 ne aka sace, kuma kudin an fitar da su ne a watan Satumba zuwa wasu asusu biyu da ke Japan da Biritaniya.
Jaridar ta kara da cewa wannan satar an yi ta ne "ta hannun ma’aikatan bankin," kuma an riga an gudanar da tambayoyi ga wasu ma’aikata a Babban Bankin Uganda da kuma ma’aikatar kudi.
Masu bincike sun bayyana cewa suna daukar wannan batu a matsayin sata daga cikin gida. Wannan matsayi ya yi daidai da sakamakon binciken da rahoton kididdiga na Babban Bankin Uganda ya nuna.
Duk da haka, bayan faruwar lamarin, bankin ya sanar cewa ya samu damar dawo da shilingi biliyan 37 daga cikin kudin da aka sace.
Har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike kan wannan al’amari.
@Daily Nigeria Hausa