Majalisar wakilai ta najerita tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta maido da tallifin man petur

A cikin makon nan ne majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta gaggauta janye ƙarin farashin mai da na tukunyar gas.

Tun bayan da kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin mai, sau biyu a cikin wata guda, al'amura suka ƙara dagulewa a Najeriya tare da jefa ƴanƙasar cikin wani yanayi na wahala da tsadar rayuwa.

Ƙarin na kimanin kaso 15 ya zo ne bayan bayanai da suka nuna NNPCL ya zare hannunsa daga dillancin fetur tsakanin matatar mai ta Ɗangote da 'yankasuwa.

A yanzu dai ana sayar da man fetur ne a kan sama da naira 1,000 a sassan Najeriya yayin da kowane kilo na iskar gas kuma ake sayar da shi kan naira 1,500.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org