Mafi Akasarin Bindigogin Da Ke Hannun ‘Yan ta’adda Na Gwamnati Ne - Ribadu

Mafi Akasarin Bindigogin Da Ke Hannun ‘Yan ta’adda Na Gwamnati Ne - Ribadu
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya zargi wasu ‘yan sanda da sojoji da sayarwa da ‘yan ta'adda makamai ko ba su haya, irin makaman kuma da ake amfani da su wajen hallaka jami'an
tsaron.

Mallam Nuhu Ribadu wanda ke jawabi yayin gangamin lalata bindigogi kimanin 2,400 da hukumar hana yaduwar makamai ta Najeriya ta yi a wajen birnin Abuja, ya ce duk jami'in tsaron da zai sayar wa da ‘yan ta'adda makami to tabbas wannan ya wuce kidnapa ko dan Boko Haram.

Dama dai an dade ana zargin wasu baragurbin jami'an tsaro na sai dawa ‘yan ta'adda makamai, zargin da hukumance mashawarcin shugaban kasa kan tsaron ya tabbatasr da shi.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org