Red Cup Day ta koma Red Strike Day — Ma’aikatan Starbucks sun aika sako mai zafi ga duniya.cikakken bayani👇
A Amurka, Ć™ungiyar ma’aikatan Starbucks ta gudanar da babban yajin aiki a ranar Alhamis — wato dai ranar da kamfanin ke shahara da Red Cup Day, wanda ke jawo dubban kwastomomi zuwa shagunan su.
Rahotanni sun nuna cewa ma’aikata a wurare da dama sun tsaya cik, suna zargin kamfanin da kin kyautata yanayin aiki, rashin adalci a cikin tsarin albashi, da kuma matsalolin tsaro da suka dade suna jan hankali a kai.
Abin ya kara zafi ne bayan zoĆ™arin sabon shugaban birnin New York, Zohran Mamdani, wanda ya fito karara ya goiyi bayan ma’aikatan, yana kiran kwastomomi da su guji sayayya a ranar, don nuna goyon baya ga yajin.
Wannan yajin ya jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, inda masu goyon bayan ma’aikatan ke cewa Starbucks na bukatar “ta fara mutunta ma’aikacinta fiye da kofunan ja.”