Mummunar Hadari a Tekun San Diego — Jirgin ƴan hijira ya kife, mutane huɗu sun mutu.karin bayani👇


Hukumar Tsaron Teku ta Amurka (U.S. Coast Guard) ta tabbatar da rasuwar mutum huɗu bayan wani ƙaramin jirgin da ake zargin ya ɗauki ‘yan hijira ya kife a kusa da San Diego, California.

Wannan ya faru ne bayan rahotannin da suka nuna cewa an ga kananan jirage biyu suna kokarin sauka da daddare, kafin ɗaya daga cikinsu ya ci karo da guguwa ya kife.

Jami’an ceto sun isa wurin cikin hanzari, inda suka ceto wasu mutane, amma suka tabbatar da cewa mutum huɗu sun rasa rayukansu. Har yanzu ana bincike kan adadin waɗanda ke cikin jirgin da asalin su.

Hukumar Coast Guard ta bayyana cewa yankin San Diego na kara zama mahada mai hadari saboda yawan shige-da-fice ta ruwa, kuma za a kara tsaurara matakan tsaro a yankin.


#kindness #lovestory #hope #fblifestyle #DanmasaniRadio #whiteConnectGL #Darussalam
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org