Majalisar Dinkin Duniya ta zartar da sabon ƙuduri kan take hakkin ɗan Adam a Iran —
Kwamitin na Uku na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA Third Committee) ya amince da wani muhimmin ƙuduri a ranar Laraba wanda ya la’anci tarihinmna take hakkin ɗan Adam da gwamnatin Iran ke yi.
Rahoton ya kunshi korafe-korafe da suka shafi tsare-tsaren siyasa, kame ‘yan adawa, takura wa mata, da cin zarafin fursunoni.
UN Special Rapporteur kan hakkin ɗan Adam a Iran ya yaba wannan matakin, yana cewa ƙudurin wani muhimmin saƙo ne na duniya cewa babu wata ƙasa da za ta kauce wa alhakin kare ‘yancin ɗan Adam.
Iran dai ta yi watsi da zarge-zargen, tana cewa ƙudurin siyasa ne kuma ba ya nuna ainihin yanayin da ke ƙasarta.
#UN #Iran #HumanRights #UNResolution #GlobalRights #InternationalJustice #DanMasaniRadio #WhiteConnectGL #Darussalam