Majalisa ta shiga tsakanin Wike da matashin soja — Sanata Lawan ya ce wannan rikici ba za a barshi ya lalace ba! cikakken labarin 👇


Sanata Ahmed Lawan: Majalisa Za Ta Saka Hannu a Rikicin Wike da Matashin Sojan Abuja

Sanata Ahmed Lawan, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya bayyana cewa majalisar dattawan Najeriya za ta shiga tsakani domin warware rikicin da ya barke tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da matashin jami’in soja, Laftanal Yerima, wanda ya jawo cece-kuce a fadin Æ™asar.

A yayin zantawa da manema labarai, Sanata Lawan ya ce:

Wannan batu ba abu ne da za a yi watsi da shi ba, domin yana da nasaba da martabar gwamnati da kuma dangantakar jami’an tsaro da jami’an siyasa.

Ya ce majalisar za ta jirgi bayanai daga bangarorin biyu, sannan ta gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da adalcI.

Sanata Lawan ya kara da cewa matsalar ba kawai rikici ba ce; tana da alaka da dokar amfani da filaye, tsaro, da kuma iyakar ikon jami'an gwamnati a birnin tarayya.


Ya jaddada cewa majalisa tana da rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da mutunta doka, kuma za ta yi aiki domin gujewa matsalolin da ka iya rage martabar jami’an tsaro ko gwamnati.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org