Google na kokarin kauce wa rarrabawa daga harkar talla yayin da shari’ar antitrust ta kusa kammaluwa.
A yayin da shari’ar antitrust da gwamnatin Amurka ta shigar kan Google ta kai matakin ƙarshe, kamfanin na ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a raba masa sassan harkar tallan dijital ba.
Gwamnatin Amurka na zargin Google da mamaye kasuwar tallace-tallacen online ta hanyar amfani da damar da yake da ita a injin bincike da kuma tsarin saye-da-sayar da tallace-tallace. Masu shigar da ƙarar sun ce matsayinsa ya zama kamar ƙofar da ba’a iya wucewa ga sauran ‘yan hamayya.
Google ta dage cewa tsarin ta ba ya tauye gasa, kuma rarraba kamfanin zai iya haifar da tashin hankali a kasuwar fasaha, ya karya tsarin da ake dogaro da shi wajen biyan mawallafa da kasuwanni.
Ana sa ran alkalin da ke jagorantar shari’ar zai yanke hukunci a watanni masu zuwa, wanda zai iya kasancewa daya daga cikin manyan hukuncin antitrust da suka taba fuskantar kamfanin fasaha a wannan ƙarni.
#Google #Antitrust #TechTrial #DigitalAds #USDOJ #BigTech #CompetitionLaw #BreakingNews