— Gamayyar ma’aikatan lafiya sun ce Gwamnati ta watsar da su, albashi ya tsaya, sharuɗɗan aiki sun lalace.Yajin aiki zai fara ba tare da ja da baya ba.bayani 👇
Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya na Najeriya (wanda ya haɗa da NMA, NANNM, JOHESU da sauransu) sun sanar da cewa za su fara yajin aiki daga gobe Asabar, 15 ga Nuwamba 2025.
Sun ce ba su da wani zaɓi face yajin aikin ne saboda:
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da buƙatunsu tsawon watanni.
Gyaran tsarin albashi ba a kammala ba, kuma dukkanin alkawuran da gwamnati ta yi ba a aiwatar da su ba.
Tsarin aiki yana da rauni: ƙarancin kayan aiki, rashin tsaro ga ma’aikatan asibiti, da wahalhalu wajen kula da marasa lafiya.
Ma’aikatan sun ce Gwamnati ta kasa biyan kuɗin alawus, ta kasa aiwatar da sabon tsarin kwangila, kuma ba ta ɗaukaka matsayinsu na ƙwararru yadda ya kamata ba.
Ƙungiyoyin sun gargadi cewa yajin aikin zai ci gaba har sai an biya hakkokinsu, kuma sun roƙi jama’a su fahimci cewa matakin domin kare martaba da jin daɗin ma’aikatan lafiya ne.