A gaban kotu, wata tsohuwa ce ke tsaye Helen siririya, sanye da rigar asibiti ce a jikinta. Kuma, abin bakin ciki, hannuwanta a cikin sarƙa.shiga nan don samun cikakken labarin 👇


Shekarunta 91.An kama ta da zargin sata.Ee, sata.Amma ba irin satar nan ta rashin kunya ba — a’a, wata sata ce da ta fito daga radadin zuciya.Helen da mijinta George sun shafe shekaru 65 suna rayuwa tare. George, mai shekaru 88, yana fama da matsanancin ciwon zuciya. Magani ne kaɗai ke riƙe numfashinsa.Amma suna rayuwa ne a yanayin rashin kuɗi. Kuma a watan da ya gabata… inshorar da suke dogaro da ita ta ƙare saboda sun kasa biya.Da Helen ta je ɗaukar maganin mijinta, farashin ya tashi daga $50 zuwa $940.Ta tsaya kallon takardar kuɗin… ta kasa cewa komai.Ta koma gida ba tare da magani ba.Na tsawon kwanaki uku, ta zauna tana kallon mijinta yana wahalar numfashi. Yana neman taimako. Yana neman agaji.Rana ta huɗu, zuciya ta yi mata nauyi. Ta ɗauki shawarar da bai kamata ba, amma cikin hali ba za ka ce ba.Ta je inda ake saida magani, ta ɗauki maganin a ɓoye.Ba ta kai ƙofar fita ba, aka tare ta. Aka kira ‘yan sanda suka kama ta.A lokacin shigar da bayanan kama ta… jinin ta ya hau sama sosai har ta fadi. Aka garzaya da ita asibiti.Washe gari, da rigar asibiti, har yanzu cikin rashin lafiya take, aka kawo ta gaban kotu.Da aka tambaye ta, cikin ƙasa da murya ta ce:“Ban san abin da zan yi ba… shi ne kaɗai nake da shi.”Kotu ta yi shiru.Alƙalin ya kalle ta sosai — ba laifi yake gani ba, amma ƙunci.Ba mugunta yake gani ba, amma gazawar tsarin kula da marasa galihu.Sai ya ce:“Ku cire mata sarƙa. Wannan ba mai laifi ba ce. Wannan kuskuren tsarinmu ne.”Alƙalin ya kori shari’ar a nan take, ya kuma ba da umarnin a samar musu da tallafi da kulawa cikin gaggawa — ga Helen, ga George, ga rayuwar da suka ciyar a tare tsawon shekaru 65.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org