Yawan jami’an sojin da ake tsare da su bisa zargin shirin juyin mulki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun kai mutum Arba'in da biyu.
Hedikwatar Tsaron Najeriya ta farko ta sanar da kama jami’ai 16 bisa abin da ta kira matsalolin ladabtarwa, ba tare da ta danganta lamarin da juyin mulki ba.
Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa an kama su ne bisa zargin shirin kawo cikas ga tafiyar mulkin dimokuraɗiyya da Najeriya ta shafe shekaru 26 tana yi ba tare da katsewa ba.
Majiyoyin tsaro da suka tattauna da jaridar Daily Trust sun bayyana cewa ana ci gaba da yi wa jami’an tambayoyi domin gano irin rawar da kowannensu ya taka da kuma yadda shirin ya kai.
“Har yanzu mutum 42 aka kama. Ana yi musu tambayoyi don gano yadda suka shiga cikin lamarin, da kuma ko akwai wani tsari na ainihi da ya wuce tattaunawa kawai,” in ji wata majiya.
Wata majiya kuma ta bayyana cewa yawan kamun na iya ƙaruwa yayin da Hukumar Leken Asirin Tsaro (DIA) da Rundunar ‘Yan Sandan Soji ke ci gaba da bibiyar hanyoyin sadarwa da kuma binciken tushen kuɗin da aka yi amfani da su.
A halin yanzu, mai ba wa Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasa na goyon bayan matsayar hukumomin tsaro kan lamarin.
Yayin wata hira da tashar TVC, Dare ya ce Rundunar Sojoji ita ce cibiyar da kundin tsarin mulki ya ba ikon kare ƙasar da tabbatar da haɗin kai da tsaron iyakokinta, tare da jaddada cewa gwamnatin Tinubu na da cikakken tabbaci game da amincin rundunar.
“Za mu tsaya kan bayanin da sojoji suka bayar, domin su ne tsarin mulki ya ba su ikon kare ƙasar nan,” in ji Dare. “Sai dai idan rundunar soji ta fito da wani sabon bayani, mu za mu tsaya kan na yanzu.”
Wani masani kan harkokin tsaro kuma tsohon jami’in soja, Bashir Galma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na iya ƙin tabbatar da zargin juyin mulki a bainar jama’a don kauce wa tayar da hankula ko tsoratar da masu zuba jari.
Sai dai ya gargadi cewa yin watsi da gaskiya fiye da kima na iya lalata amincewar jama’a idan daga baya aka samu hujjoji masu karfi.
