Shekaru 2 a kan Mulki: Buhari ya jinjinawa Tinubu tare da yin kira da 'yan Nijeriya su kara hakuri
Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru biyu a kan mulki, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin jam’iyyar APC baya tare da kasancewa masu kyakkyawan fata kan makomar kasar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, Buhari ya yaba da irin jagorancin da Tinubu ke yi, inda ya jaddada cewa ko da gwamnati da jam’iyya na da dalilin murna, jagoranci tafiya ce mai dogon zango wadda ke bukatar hakuri da jajircewa.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke kokarin aiwatarwa suna da matukar muhimmanci, amma ba za su haifar da sakamako cikin dare daya ba. Ya yi gargaɗi cewa kada a bar rikice-rikicen siyasar cikin gida su hana nasarar wadannan gyare-gyare.
“Ina goyon bayan kokarin gwamnatin na yaki da talauci da hauhawar farashi, wadanda suka fi shafar talakawa,” in ji Buhari. “Amma wannan aiki babba ne sosai kuma ba gwamnati kadai za ta iya ba. Dole ne bangaren masu zaman kansu da mu duka a matsayin 'yan kasa mu bada gudummawa ta hanyoyin da muke iya yi.”
Ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu fata da kwarin gwiwa kan makomar kasa, yana mai cewa:
“Kar mu yi wa gwamnati manyan tsammanin da za su zama nauyi,” in ji shi.
Buhari ya kammala da mika gaisuwar taya murna ga Shugaba Tinubu, yana cewa: “Ina mika sakon taya murna da fatan alheri ga Shugaba Tinubu a cikar sa shekaru biyu a ofis. Allah ya ci gaba da ba ka hikima da kulawa wajen jagoranci.”