Ƴansanda sun fara binciken yadda wani malami ya lakaɗawa wani ɗalibi a Adamawa
Rundunar ƴansandan Jihar Adamawa ta ce za ta gudanar da bincike kan wani malami a makarantar Aliyu Mustafa da ke Jimeta da ake zargi ya azabtar da wani dalibi mai suna Jaafar Bashiru saboda kawai ya ci mangwaro a harabar makarantar.
A cewar shaidun gani da ido, malamin ya farfasa tare da kumbura wa yaron jiki da duka.
Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da aka fito cin abinci a makarantar lokacin da malamin ya kama Jaafar yana cin mangwaro.
Mahaifin Ja’afar, Bashiru Haman, wanda ya zo makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar dansa, ya kadu matuka da ya ga an yi wa dan nasa dukan tsiya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kaddamar da bincike kan lamarin.
Kwamishinan ‘yan sanda, Dankombo Morris, ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da ɓangaren bincike, da ya gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin.