Kotu ta tura tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zuwa Gidan Yarin Kuje kan almundahanar Naira biliyan 110.4.

 Mai Shari’a Maryann Anenih ta Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya ta ki amincewa da bukatar beli da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya shigar, tana mai cewa an gabatar da bukatar ne ba a kan lokaci ba.

A yayin yanke hukuncin,  Mai Shari’a Anenih ta bayyana cewa bukatar ta rasa cancanta saboda an shigar da ita ne yayin da wanda ake tuhumar bai ke a tsare ba kuma ba a gurfanar da shi gaban kotu ba.


Tsohon gwamnan yana fuskantar shari’a tare da wasu mutane biyu kan zargin halatta kudaden haramun na Naira biliyan 110 da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gabatar a kansa.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org