Wasu Yan Mata Sun Damfari Wani Dan Kasuwa Wayar Salula Ta Naira 970k Ƙirar Iphone
Ɗazu da yamma wasu mata guda biyu sukazo shagon Wani Membanmu da zummar zasu sayi waya ƙirar IPhone 13pro max. Bayan sunzo sun sameshi a shago yabasu wuri suka zauna sukace sunzo siyan waya IPhone 13pro max sabuwa.
Sai yace Bashi da sabuwa sai second, sai sukace sudai Sabuwa sukeso Seal acikin kwali, sai yaje shagon maƙocinsa ya dakko musu sabuwar, da zuwa sukayi ciniki suka gama, sai suka amshi account number ɗinsa suka tura wai za'a tura masa da kuɗin.
Dama awajen shagon suke azaune sai ɗayar tace tanaso tashiga cikin shagon ta zauna saboda akwai wanda bataso ya ganta, sai yabata waje tashiga ciki ta zauna, Ashe akwai wani Exactly irin kwalin wayar a hanunta, shigarta Shagon keda wuya Ta ɗauke waccan wayar Mai kyan wacce ya karɓo ita kuma ta ajiye wannan Abun Da Kuke Gani.
Sai tace bari Suje sudawo kafin aturo da Kuɗin, Haka suka tafi da wayar Dubu 970k suka Ajiye Masa Wannan Qasar Da Kuke Gani😥, bai tashi sani ba sai da yaga sun daɗe basu dawo ba sai yace bari yaje ya mayarwa masu wayar da ya Amso Idan Sun dawo Sai yakoma ya karɓo musu😥.
Yana ɗagawa yaji ba yadda yasaba ji ba, kawai yafara salati, yana buɗewa yaga ƙasa ce acikin kwalin sukayi Wrapped ɗinta haka, Sun tafi da asalin Wayar😥. Kuma abun takaici Wanda sukayi wannan aika aikan Hausawa ne😥, Sun tafi sun barshi batare da sunyi tunanin halin da zai shiga ba😥, Yanzu dai munfara yin ƙoƙarin Ɗaukar Matakan Da Suka Dace.
Allah Katona Musu Asiri, Allah Yabi masa Haƙƙinsa, Jama'ar mu kuyi Hattara🙏🏿!.