Shugaban Sojin Kasa Lieutenant General Olufemi Oluyede, ya Bukaci Dakarun Sojin Kasar nan Dake arewa Maso Gabashin Kasar nan da su Kara kaimi Wajen Fatattakar Yan Boko Haram

 Ya bayyana Hakan Yayi Wata Ziyara da ya Kai wa Dakarun a sansanonin su Daban Daban Dake Maiduguri a arewa Maso Gabashin Kasar nan.

Da yake Yi Musu Jawabi Yace zai Tabbatar da Walwalar Dakarun da Kuma Samar Musu da Kayan aiki da Suke Bukata Wajen Fatattakar Yan Boko Haram harma ya yaba Musu Bisa Sadaukarwa da Suke Wajen Gudanar da aikinsu.

Haka Kuma lieutenant General Oluyede ya Kai Ziyara asibitin Sojin Dake Maiduguri domin Duba Lafiyar Sojin da Suka Samu rauni a Wajen Yaki da Yan bindigar na Boko Haram.

Jaridar Nigeria 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org