Gasar Firimiya ta Ƙasa: Pillars ta doke Katsina United 1-0 a wasan hamaiya

 Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars ta doke takwararta ta Katsina United 1-0 a wasan hamaiya a tsakaninsu.

Ɗan wasan gaba, Abba Adam , wanda aka fi sani da Oscar nenya jefa ƙwallon tun a minti na 34 da take wasan, inda kwallon ɗaya tilo ta makale har zuwa lokacin tashi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a jihar Kano.

Sai dai kuma DAILY NIGERIAN HAUSA ta gano cewa wasan ya bar baya da ƙura bayan da fadan daba ya tashi bayan wasan.

Wasu ganau sun shaida mana cewa a kan tashi daga wasan sai aka ga matasa su na ta zare muggan makamai su na yin kan jama'a, lamarin da ya haifar da guje-guje a yankin filin wasa na Sani Abacha .

"Wallahi ina kan babur na kusa zuwa Kofar Mata, sai na ga ana ta gudu. To ban tsaya ba sai ma ci gaba da tuƙi, ai kuwa ina zuwa daidai junction  din Kofar Mata kawai sai naga daruruwan matasa da makamai su na kokarin sarar juna.

"Na rasa ya zan yi, sai na yi sa'a na shiga jikin wata motar kurkura, nan na yi sa'a mu ka wuce lafiya," in Lawan Fagge, mazaunin birnin Kano.

A cewar wani mai goyon bayan Pillars, Habu Idris, wai su yaran sun ci alwashin cewa sai sun far wa magoya bayan Katsina United ko da Pillars din ta lashe wasan.

A cewar wani  mai suna Ibrahim Barau, "wallahi da ido na na ga yaran sun wuce da makamai a cikin buhu.

"Da bakin kwari zan ke na ciri kudi a bankin UBA, sai na fasa na wuce zuwa Bello Road na fita a can,"

DAILY NIGERIAN HAUSA ta gano cewa lamarin ya jefa al'umma da dama cikin fargaba da tinziri, inda ƴan kasuwar Kantin Kwari su ka riƙa rufe shaguna tun kafin a tashi daga wasan.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org