An dinkira ma Wani magoyin bayan Arsenal harsashi yayin murnar cin Man Utd
Ana zargin cewa wani jami'in tsaro ya harbe wani magoyin bayan Arsenal a Uganda, lokacin da yake murnar nasarar da ƙungiyarsa ta samu kan Manchester United a gasar Firimiyar Ingila ranar Laraba.
An kuma jikkata wani yayin da jami'in tsaron ya buɗe wuta kan dandazon muagoya bayan Arsenal da ke murna a wani wajen cin abinci a garin Lukaya, mai nisan kilomita 100 da Kampala babban birnin ƙasar.
Lamarin ya faru ne ana daf da kammala buga wasan, wanda Arsenal ta samu nasara da 2-0.
Wani ɗan jarida a yankin ya faɗa wa BBC cewa mai kula da wajen da ake kallon wasan ya fusata da irin hayaniyar da magoyan Arsenal ɗin ke yi, inda ya buƙaci jami'in tsaron da ya ɗauki mataki.
Sai dai mutanen ba su saduda ba, inda suka ci gaba da murna da sowa.
Wani shaida ya faɗa wa ɗan jaridar cewa, mai wajen cin abincin da kuma ake kallon wasan ya kashe injin da ke bayar da hasken wuta a wajen, abin da ya fusata masu kallon har ta kai suka ƙara ihu fiye da farko.
A lokacin ne kuma ake zargin mai gadin wurin ya buɗe musu wuta.
An ruwaito cewa wanda lamarin ya rutsa da shi John Ssenyonga, mai shekara 30, ya mutu nan take a wajen.
An kuma garzaya da wani magoyin bayan Arsenal ɗin Lawrence Mugejera zuwa asibiti bayan samun raunuka.
Mai gadin da kuma manajan da ke kula da wurin sun tsere bayan faruwar lamarin, inda jamin'an tsaron ke ci gaba da farautarsu.
BBC HAUSA