Zargin Hannu A Ta'áddãɲci: Ƙungiyar (RCDO) Ta Buƙaci Gwamnatin Ƙasar Amurka Ta Haramta Wa Sanata Shehu Buba Shíga Ƙasar

Ƙungiyar fararen hula da ke fafutukar samar da cigaba a yankunan karkara, wato "Nigerian civil society organisation, the Rural Community Development Outreach (RCDO), ta buƙaci ƙasar Amurka ta harámta wa Sanatan Bauchi ta Kudu, ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC, Sanata Shehu Buba, shiga ƙasar, sanádiyyar zargiɲ hannu cikin ayyukan ta'addáɲci da ake masa.


Ƙungiyar ta nemi wannan buƙata ne ta cikin wata takarda da ta aike wa ofishin jakadancin ƙasar mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Ikenna Ellis Ezenekwe, inda ta bayyana cewa ana tuhumar sanatan da hannu cikin ɗaukan nauyin ta'addanci wanda tuni rundunar tsaron faríɲ kaya ta (DSS) ke cigaba da bincike, kamar yadda jaridar (Pulse) ta bayyana.

"Mun ga yadda ta'áddâɲcí ya lalata Najeriya musamman ma yankin Arewa maso Gabas, da ƙauyukanmu, sama da shekaru 17 baya. Idan har wannan zárgi ya zama gaskiya, wakilin al'umma ya ci amanar ƙasa". Inji ta.

Ƙorafin ya ƙunshi cikakkun bayanai har da yadda jami'aɲ DSS suka gudanar da sumame a Jihar Bauchi suka kama wani mai suna Abubakar Idris wanda ake tuhuma da ayyukan ta'áddaɲcí a lokacin da yake ƙoƙarin tafiya aikin Hajji ƙasar Saudiyya.

Sai dai rahoton Arise TV ya bayyana cewa binciken DSS bai gano ko ofishin sanatan na da alaƙa da shirin tafiyar Idris ɗin ba ko a'a, inda suka yi nuni da cewa amma dai ɗaya daga cikin ma'aikatan sanatan ne ya shirya takardun fitar Idris ɗin.

"Wannan bayanai sun tabbatar da ayar zargi duba da céwa Sanata Buba shi ne shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalissar ƙasa". Ƙungiyar ta RCDO ta ƙara da cewa tayaya za mu tabbatar da cewa muna da tsaro a ƙasa alhalin tsaron na hannun wanda ake tuhuma".

Dan haka ne ƙungiyar ta nemi ƙasar Amurka da ta haramta wa sanatan shiga ƙasar zuwa wani lokaci domin ba da damar gudanar da bincike.

Ƙungiyar ta kuma ƙara da sukar gwamnatin tarayya inda ta zargi shugaba Tinubu da shugaban majalissar dattijai, Godswill Akpabio da yin shirin kan lamarin duk da cewar suna sane da tuhumar da DSS ke yi. "yin adalci tun daga matakin sama shi nr abin da ya kamata matuƙar muna son zaman lafiyar ƙasar". Ƙungiyar ta ce.

#Dokin karfe Photos Dokin karfe TV
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org