Takaitaccen Tarihin Jarumin Finafinan India, Amrish Puri (Mogambo)

 


Daga Muhammad Cisse

Shimfida 

Daya daga cikin fitattun ’yan fim din Indiya da suka taka muhimmiyar rawa shi ne marigayi Amrish Puri, wanda aka fi sani da lakanin Mogambo.…Amrish Puri ɗan film din Indiya ne, wanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mutane a fina-finan Indiya da wasan kwaikwayo. Ya yi fina-finai sama da 450, tsakanin 1967 zuwa 2005, ya tabbatar da kansa a matsayin daya daga cikin fitattun tsakanin jaruman fina-finan Indiya. Ana tunawa da Puri saboda rawar da ya taka a nau'ikan fina-finai daban-daban,

 musamman muguta (Boss) a cikin fina-finan Hindi, da kuma fina-finan duniya. Ya fito a sarki mai mugayen ayyuka a cikin fina-finan 1980s da 1990s, keɓaɓɓiyar muryarsa ta sa ya yi fice a cikin sauran basawan zamanin. Puri ya lashe lambar yabo ta Filmfare a matsayin mafi kyawun jarumi. 

Haihuwa 

An haife shi ne a garin Nawanshehar da ke gundumar Punjab, Indiya, a ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 1932. Sunan mahaifinsa Lala Nihal Chand, mahaifiyarsa kuma, bed Kaur. ’Yan uwansa, Chaman Puri da Madan Puri, dukkansu ’yan fim ne su ma.

Karatu 

Bayan ya kammala karatunsa a Kwalejin B. M. da ke birnin Shimla, ya tafi zuwa birnin Bombay (Mumbai a Yanzu) da nufin fara fitowa cikin fina-finai. Tashin farko da aka yi masa jarabawa a wannan fanni, sai ya fadi, wanda haka ya sanya ya kama aiki da wata ma’aikatar Inshorar Ma'aikata ta Gwamnatin Indiya. Kasancewar yana da sha’awa ta musamman ga harkar fim, sai ya fara fitowa a wani fim da kamfanin Prithbi Theatre ya shirya, mai suna Prem Pujari kuma tun daga wannan lokaci ya fara aikin fim gadan-gadan.

Fitowa a matsayin 

Wasu daga cikin fina-finan da ya fito a cikinsu sun hada da: Kachchi Sadak, Mumbai Edpress, Kisna: The Warrior Poet, Ab Tumhare Hawale Watan Saathiyo, Hulchul, Aitraaz, Taarzan: The Wonder Car, Mujhse Shaadi Karogi, Lakshya, Deb, Woh Tera Naam Tha, Dil Pardesi Ho Gayaa, Out of Control, Jaal, The Hero, Khushi, Rishtey, Jaani Dushman, Shararat Badhaai Ho Badhaai, Nayak, Yaadein, Gadar, Mujhe Kucch Kehna Hai, Chori Chori Chupke Chupke, Censor, Zubeidaa, Mohabbatein, Dhaai Akshar Prem Ke, Badal, Shaheed Uddham Singh, Thakshak, Gair Baadshah, Taal, Jai Hind, Jhooth Bole Kauwa Kaate, China Gate, Doli Saja Ke Rakhna, Koyla, Dhaal, Himalay Putra, Pardes, birasat, Ghatak, Diljale, Kala Pani, Dilwale Dulhania Le Jayenge, Hulchul, Karan Arjun, Droh Kaal, Tejasbini, Gardish, Damini, Suraj Ka Satban Ghoda, bishwatma, Tehelka, Phool Aur Kaante, Ghayal, Nigahen, Waaris, Shahenshah, Mr India, Loha, Nagina, Mashaal, Coolie, Gandhi, Manthan, Hulchul, Reshma Aur Shera, da sauransu.

A matsayinsa na dan fim, ya ci zamaninsa cikin nasara, musamman yadda ya rika samun kyaututtukan yabo daban-daban. Misali, ya taba samun kyautar yabo ta mujallar Filmfare, inda suka zabe shi a matsayin fitaccen mataimakin jarumi, da fina-finansa na Meri Jung da Ghatak da kuma birasat. Haka kuma ya samu kyauta a bikin fina-finai da aka gudanar a birnin Sydney na kasar Australia, inda aka zabe shi saboda kokarin da ya yi a fim din Suraj Ka Satban Ghoda.  

Amrish Puri ya taba cin kyautar Kwalejin Sangeet Natak bisa la’akari da abin da ya yi cikin fina-finansa. Ya samu fita sarari a sana’ar fim ne tun yana dan shekara arba’in a duniya, musamman da fim din farko da ya fara fitowa cikinsa mai suna Reshma Aur Shera, duk da cewa ba shi ne fim dinsa na farko da ya fara fita kasuwa ba, domin kuwa fim dinsa na farko da jama’a suka fara gani, shi ne Prem Pujari.

Jarumin ya saba fitowa ne a matsayin mamugunci a fina-finai. Ya fara fitowa a wannan matsayi a fina-finan Nishant da Manthan da Bhumika da kuma Suraj Ka Satban Ghoda. Ya samu lakanin Mogambo ne a lokacin da ya fito da wannan suna a fim din Mr. India a shekarar 1987, wanda Shekhar Kapoor ya ba da umurni. Sai dai ba dukkan fina-finansa ne ya fito mugu ba, akwai fina-finan da ya fito a wani matsayin na daban, musamman ma fina-finai kamar: Pardesh da Gardish da Chori Chori Chupke Chupke da kuma Dilwale Dulhaniya Le Jayenge.

Wani abin da ya kara jan hankalin masu kallo ga Amrish Puri shi ne, tun wani lokaci da ya yi askin kwal-kwabo, domin daukar shirin fim din Amurka na Indiana Jones, inda ya fito a matsayin mamugunci, da sunan Mola Ram da kuma fim din Temple of Doom. Ganin yadda abin ya yi armashi, sai kawai ya ci gaba da barin kansa a aske, kuma ya kafa tarihi a matsayin fitaccen dan wasan da ke fitowa a matsayin mugu, a fina-finan Indiya.

Wani hali da ya tarkata kuma shi ne, yana da sha’awar zagayayyar hular nan ta kaboyi, inda aka ce kafin rasuwarsa, ya tara irin wadannan huluna har sama da dari biyu. An ce duk lokacin da ya samu tafiya wata kasa, sai ya sayi irin wanan hula guda biyu ko ma fiye da haka.

Shi mabiyin addinin Shiba ne, wanda aka ce mai kokari ne sosai a wannan addini. Fim dinsa na karshe shi ne Kisna: The Warrior Poet, wanda aka saki kasuwa kwanaki kadan da rasuwarsa. Ya dai rasu ne da misalin karfe 7.30 na safe a ranar 12 ga watan Janairu, na shekarar 2005. Yana da shekaru 72 a duniya. 

An kai gawarsa gidansa domin mutane su yi gaisuwar ta karshe, kuma an yi jana’izarsa a ranar 13 ga Janairun 2005 inda aka kone gawarsa a Shivaji Park. 

Iyali

Ya auri Urmila Divekar a ranar 5 ga Janairu 1957, a wajen ibadar Shri Krishna a Wadala. Ma'auratan suna da 'ya'ya biyu, ɗan namiji Rajeev Puri da 'ya mace Namrata Puri. Ɗansa Rajeev ɗan kasuwa ne. Yana da jikoki hudu, Sachi, Harsh Vardhan, Shantanu Bagwe da Krish Bagwe.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org