Shugaba Ya Nuna Farin cikinsa Da Sabon Rahoton Bunkasar Tattalin Arzikin Najeriya

 A jiya ne wasu sabbin alkaluma suka nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.46% a zango na uku.

Wannan ci gaban ya zarce na 3.19% da aka fitar a zango na biyu wanda hakan ke nuna cewa ƙasar na murmurewa daga masassarar tattalin arzikin da ta yi fama da shi.

Shugaba Tinubu  ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin ci gaba da samar da ingantacciyar hanyar tattalin arziki, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa na ci gaba da jajircewa wajen kyautata rayuwar jama’a. 

Shugaban ya kuma sake jaddada alkawarinsa na kara haɓaka tattalin arzikin kasar a farkon shekarar 2025 da kuma samar da manyan sauye-sauye a sassa daban-daban.

Bangarorin da suka samar da sabbin alkaluman ci gaban GDP a wannan zangon sun hada da Noma, Sufuri, Ilimi, kiwon Lafiya, harkar gine-gine, hada-hadar Kuɗi, Inshora, fasaha, Cinikayya, da kuma  Masana'antu.

Ga Jadawalin Lissafin kamar haka:

- *Noma*: 28.65%

- *ICT*: 16.35%

- *Ciniki*: 14.78%

- *Masana'antu*: 8.21%

- *Danyen Mai*: 5.57%

- *Kudi & Inshora *: 5.51%*

* *Estate*: 5.43%*

Gwamnatin Shugaba Tinubu na da burin ganin ta cimma nasarar tattalin arzikin dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030, kuma tana kokarin rage harajin da ke kan kananan ‘yan kasuwa da inganta daidaito ta hanyar yin garambawul a bangarorin kudaden shiga.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org