Kuskuren da Su Malam Kabir Gombe da Ahmad Suleman Sukai A Garin Kano.
Inji Datti Assalafi da ya ce.
Ni a fahimtata Sheikh Kabiru Gombe da Alaramma Ahmad Ibrahim Suleman Kano sun yi babban kuskure da suka halarci bikin Dinner wanda aka hada maza da mata da 'yan siyasa
Tsakani da Allah ko kadan ban ji dadin faruwar hakan ba, wannan zai bude kofar barna mai girma a duniyar Sunnah da muke yinta a Nigeria
Matsayin da Sheikh Kabiru Gombe yake da girman darajansa ya wuce zuwa irin wannan guri, domin a kullun Malamai abin koyi ne don haka dole su kasance masu kiyaye mutuncin kansu
Idan gama garin mutane irin mu muka halarci guraren biki irin wannan ba zai zama abin aibi ba, amma Malami wanda duniya ta sanshi a fagen Karantar da Sunnah yafi karfin zuwa gurin nan ko me za'a bashi
Allah Ka bamu ikon gyara kuskuren mu