Kotu ta ci gwamnatin Katsina da SIEC tarar ₦300,000 kan ƙin zuwa sauraren ƙarar da SDP ta shigar game da zaɓen ƙananan hukumomi na 2025
Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia
Wata babbar kotun tarayya dake Katsina ta ci gwamnatin Katsina da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (SIEC) tarar Naira dubu Ɗari Uku (₦300,000) a sakamakon rashin bayyana a gaban kuliya kan ƙarar da Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) reshen jihar Katsina ta shigar dangane da zaɓen ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2025 mai zuwa.
Jam’iyyar SDP karkashin jagorancin shugaban ta na jiha, Alhaji Bello Adamu Safana, da ɗaukacin kwamitin zartarwa ne suka yi bayanin halin da shari’ar ke ciki bayan zaman kotu na ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamban 2024. Lauyoyin waɗanda ake ƙarar dai ba su halarci zaman kotun ba, lamarin da ya sa alkalin kotun ya umarci su biya kuɗin a matsayin diyyar rashin bayyanar su a gaban kuliya.
Kotun dai ta dage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba, 2024, biyo bayan ɗage sauraren ƙarar da kuma rashin halartar waɗanda ake ƙara. A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Sakataren jam’iyyar SDP, Mustapha Mohammed Kurfi ya bayyana cewa, jam’iyyar ta fara ɗaukar matakin shari’a ne domin ƙalubalantar wasu sharuɗɗan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina ta gindaya ga ƴan takara domin shiga takarar zaɓen ƙananan hukumomi na 2025, wanda jam’iyyar SDP ta ga ya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Jam’iyyar SDP ta jaddada ƙudirinta na tabbatar da tsarin dimokuradiyya da tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe a jihar Katsina. Wakilan jam’iyyar na jam’iyyar na ci gaba da bibiyar shari’ar a gaban kotu domin magance matsalolinsu dangane da sharuddan da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina ta gindaya.
Jaridar Hikaya ta ruwaito cewa, shugaban jam’iyyar SDP na jihar, Alhaji Bello Adamu Safana, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan rashin halartar lauyoyin waɗanda ake ƙara a zaman kotun, inda ya yi na'am da matakin da alƙalin kotun ya yanke na hukunta su kan rashin bayyanar su. "Jam’iyyar SDP ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci da daidaito a harkar zabe," in ji shi.
Tawagar lauyoyin jam’iyyar SDP na shirye-shiryen gudanar da zaman kotu na gaba da aka shirya yi a ranar 27 ga watan Nuwamba, inda za su ci gaba da gabatar da ƙarar su kan gwamnatin jihar Katsina da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina. Jam’iyyar ta ƙuduri aniyar ƙalubalantar abin da suka ɗauka a matsayin rashin adalci da rashin bin tsarin mulki wanda zai iya yin tasiri a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe na 2025.
Yunƙurin da jam’iyyar SDP ke yi na magance matsalolin da suka dabaibaye zaɓukan ƙananan hukumomi na 2025, ya nuna irin ƙudurin ta na tabbatar da gaskiya da rikon amana da shigar kowace jam'iyya cikin harkokin zaɓe. Ɗagewar da jam’iyyar ta yi na bin doka da oda ya nuna himmarsu wajen ganin cewa jam’iyyun siyasa sun samu dama daidai gwargwado wajen shiga harkokin dimokuradiyya a jihar Katsina.