Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 23 a Lebanon
Aƙalla mutum 23 ne aka kashe a wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kan wasu gine-gine biyu a tsakiyar Lebanon, wajen da aka ruwaito cewa iyalai waɗanda aka ɗaiɗaita na rayuwa a ciki, a cewar ma'aikatar lafiya a Lebanon.
Mutum 15, yawanci mata da ƙananan yara aka kashe a garin Joun sannan aka kuma kashe wasu takwas a kusa daBaalchmay.
Dukkan ƙauyukan suna a wani tsauni ne da kuma wajen yankunan da Hezbollah ke da karfi.
Sojojin Isra'ila sun ce suna duba batun hare-haren, waɗanda ke zuwa a daidai lokacin da suka ce harin ya faɗa kan shingayen Hezbollah da ke wajen kudancin birnin Beirut.