Gwamnatin Katsina ta bada tallafin miliyan ₦3.5 ga iyalan mutane 35 da ta'addanci ya rutsa da su a Jibia

 A ƙoƙarin ta na yaƙi da da ta'addanci, fashi da makami, satar dabbobi, da kuma garkuwa da mutane, tare da jaje da nuna jinkai ga wadanda lamarin ya shafa, gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa, ta sake bayar da wani tallafin kuɗi kimanin Naira Miliyan Uku da Dubu Ɗari Biyar (₦3,500,000) ga iyalan mutane Talatin da Biyar (35) da harin ƴan bindiga ya shafa a ƙaramar hukumar Jibia.

Jaridar Hausa Daily Post ta ruwaito cewa, mutanen da ba su ji kuma ba su gani ba da suka ci gajiyar tallafin kuɗaɗen sun haɗa da wani mutum 1 da ƴan bindigar suka kashe, da mutane 6 da suka jikkata, da mutane 28 da ɓatagarin suka yi garkuwa da su. Duk ƴan asalin unguwannin Ka'ida, Bachaka da ƙauyen Lanƙwasau dake karamar hukumar ta Jibia.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Katsina kan waɗanda harin ƴan bindiga ya shafa da kuma ƴan gudun hijira, Hon. Saidu Ibrahim Danja 'Kogunan Jibia' ne ya jagoranci bada tallafin a madadin gwamnatin jihar, inda a cikin jawabinsa ya bayyana kansa a matsayin wanda ya wakilci Gwamna Dikko Umar Raɗɗa domin jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

Da yake jawabi kan yadda aka tsara rabon tallafin, Kogunan Jibia ya ce, "Tun farkon fara wannan shirin zuwa yanzu, gwamnatin jihar Katsina tana bada tallafin Naira milyan ɗaya ne (₦1,000,000) ga iyalan duk wani jami’in soja ko ɗan sanda ko kuma jami'n 'Community Watch Corps' ɗin da ya rasa rai a fagen yaƙi, kuma ƴan bangar da suka rasa ana baiwa iyalan su Naira Dubu Ɗari Biyar (₦500,000) yayin da duk wani jami’in da ya jikkata da iyalan farar hula da ƴan bindiga suka kashe suke cin gajiyar Naira dubu ɗari biyu (₦200,000). Sai kuma iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su suke samun Naira dubu ɗari (₦100,000). Yayinda waɗanda suka jikkata bayan dawowarsu daga jinyar da gwamnati ke ɗaukar nauyi a asibiti, suke amfana da Naira dubu hamsin (₦50,000).


A nasa jawabin, sakataren ƙaramar hukumar Jibia, Malam Muhammad Lawal, ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina kan yaƙi da ta'addanci, ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatin na ci gaba da ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suke addabar al'umma, ya kuma jaddada cewa masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro a gwamnatin jihar Katsina ci gaba da samar da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen ƙalubalen rashin tsaro tare da ɗaukar nauyin jinyar waɗanda hare-haren 'yan bindigar ya shafa.

Ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar ta Jibia, Hon. Sirajo Ado, ya yabawa ƙoƙarin Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na tunkarar matsalolin tsaro gadan-gadan domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, ya kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta ƙara ƙaimi domin shawo kan ƙalubalen na rashin tsaro domin samun wanzuwar zaman lafiya ga mazauna birni da karkara.

Sarkin Arewan Katsina, Hakimin Jibia, Alhaji Rabe Rabi'u, ya yi godiya a madadin waɗanda suka amfana da tallafin, tare da basu shawara da su yi amfani da tallafin na kuɗi yadda ya dace. Ya kuma ce shirin tallafawa mutanen da lamarin ya shafa ya ƙara tabbatar da aniyar Gwamnatin jihar Katsina na tausayi da nuna damuwa ga iyalan mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa.

 Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na ƙaramar hukumar Jibia, a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2024, ya samu hakartar ƴan siyasa, masu riƙe da muƙamai na gargajiya, jami'an tsaro da dai sauransu.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org