Cin hanci ne yake janyo yawaitar katsewar lantarki a Nijeriya - EFCC

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zakon Kasa a Nijeriya (EFCC) ta alaƙanta yawaitar katsewar lantarki da yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a bangaren samar da lantarki na kasar.
A yayin ziyarar da Kwamitin Yaki da Cin Hanci na Majalisar Wakilai ya kai ofishin EFCC a ranar Talata, shugaban EFCC Ola Olukoyede ya bayyana cewa bincike ya gano yadda 'yan kwangila suke kawo kayayayyaki marasa inganci.

Wannan abu yana janyo yawaitar lalacewa da katsewar hanyoyin wuta na kasa wanda ke yin tasiri kan jama'a a fadin kasar.

A makon da ya gabata, manyan biranen Nijeriya da suka hada da Abuja, Lagos, da Kano sun fuskanci katsewar lantarki a karo na goma da hakan ta faru a wannan shekarar.

Rashin gudanar da ayyuka masu kyau:

Olukoyede ya fada wa kwamitin cewa "A yayin da na ke magana a yanzu haka, muna fama da matsalar lantarki. idan kuka ga wasu daga binciken da muke yi a bangaren samar da makamashi, za ku zubar da hawaye."

"Mutanen da aka baiwa kwangila na kawo kayan lantarki, maimakon su yi amfani da gejin inganci na 9.0, sai su sayo masu ingancin 5.0."

Olukoyede ya ci gaba da bayyana irin rashin inganci a manyan ayyuka da ake gudanarwa, yana mai cewar a shekaru 20 da suka wuce, kasa da kashi 20 na ayyuka ka kammala gudanarwa.

Ya jaddada cewar rashin gudanar da manyan ayyuka na cigaba ya bayar da gudunmowa sosai wajen dakile Nijeriya ta ci gaba a fannin tattalin arziki.

Badakalar cin hanci:

Shugaban na EFCC ya ce a yanzu haka akwai badakalar cin hanci da ta'annati ga tattalin arziki 20,000 da ake bincike a kai.

Olukoyede ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta bayar da fifiko ga aiki da gaskiya, keke da keke, da tabbatar da aiki da dokoki don yaki da cin hanci a bangaren makamashin lantarki.

Katsewar hanyoyin rarraba lantarki a Nijeriya abu ne ruwan dare, wanda rashin zuwa jari a bangaren ne ke janyo hakan.

Nijeriya na da ikon samar da megawatt 13,000 amma tana iya rarraba megawatt 4,000 ne kawai saboda rashin ingantattun kayan aiki, in ji hukumar.

Baya ga rashin ingantattun kayan aiki, 'yan ta'adda ma na yin zagon kasa ga harkokin samarwa da rarraba lantarki a Nijeriya.

A watan da ya gabata, arewacin kasar ya fuskanci katsewar lantarki na sama da kwanaki bakwai bayan da 'yan bindiga sun lalata hanyoyin rarraba lantarkin, in ji Kamfanin Rarraba Lantarki na Nijeriya.

#Hikaya Newspaper

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org