Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro 2, sun jikkata 5 a Jibia dake jihar Katsina

Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia to

Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai wani mummunan hari a yankin gabas maso kudancin Jibia inda suka yi kwanton ɓauna har suka yi sanadiyyar mutuwar wasu jami'an tsaro biyu.
Mutanen da ƴan ta'addar suka kashe sun haɗa da mataimakin kwamandan jami'an tsaron al'umma (KTSCWC) na ƙaramar hukumar Jibia, Bala Abubakar Lawal mai kimanin shekaru 30 a duniya; da wani jami'in Youth Security Volunteers Group, Jamilu Mai Unguwa mai kimanin shekaru 35 a duniya.
Kazalika, maharan sun samu nasarar jikkata mutane 5 a ciki har da shugaban rundunar Youth Security Volunteers Group, Malam Gaddafi Lawal, waɗanda babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Katsina kan waɗanda iftila'in ƴan bindiga ya shafa da kuma ƴan gudun hijira Hon. Sa'idu Ibrahim Ɗanja "Kogunan Jibia" ya shaida wa Jaridar Hikaya cewa yanzu haka likitoci na ci gaba da kula da lafiyar su.

Harin wanda ƴan ta'addar suka kai a ranar Alhamis da misalin karfe 9:00 na dare, ya zama abin firgici da tashin hankali ga mazauna ƙaramar hukumar Jibia, kuma wannan shi ne karo na biyu da ƴan ta'addan suka kai hari a cikin watan Nuwamban 2024.

Tun a daren da lamarin ke faruwa, Jaridar Hikaya ta sanar da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina faruwar lamarin; ya kuma ce "baturen ƴan sandan yankin na Jibia ya shirya tawagar jami'ai inda suka kai farmaki ga ƴan ta'addan, suka yi artabu har sai da ƴan bindigar suka gudu.

Washe gari da safe kuma Jaridar Hikaya ta sake tuntuɓar kakakin ƴan sandan na jihar Katsina Abubakar Sadiq Aliyu domin jin ba'asi kan lamarin, amma dai haƙa ba ta cimma ruwa ba.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org