Ka koma gida, ƴan Najeriya ba za su zaɓe ka ba - Wike ya mayar wa Atiku martani

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya faɗawa Atiku Abubakar cewa shine ƴan Najeriya suka ƙi a lokutan da ya nemi kujerar Shugabancin ƙasar nan.

Wike ya ce kamata yayi Atiku ya tattara kayansa ya koma garinsu, domin a cewarsa ya fafata zaɓe da yawa kuma ya sha kaye, don haka ƴan Najeriya ba za su zaɓe shi ba.

Da yake mayar da martani ga wasu kalamai na Atiku, yayin da yake jawabi ga mabiyansa a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, Wike ya ce: “Na ji Atiku yana cewa ƴan Najeriya sun ƙi mu. Shin na nemi Takarar shugabancin karamar hukuma ne? A'a.

Na ji Atiku Abubakar yana cewa ƴan Najeriya sun ƙi mu a Jihar Ribas. Kai da ka yi takara, ka faɗi, kenan kai ne ƴan Nijeriya suka ƙi; don haka ka koma gida."

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org