Hukumar HisbahTa Jihar Kano Ta Cika Hannu Da Kwamishinan Jihar Jigawa Kan Zagin Lalata Da Mata Aure
Hukumar HisbahTa Jihar Kano Ta Cika Hannu Da Kwamishinan Jihar Jigawa Kan Zaĝiɲ Làląta Da Mata Aúrê
Biyo bayan wani sumame da ta kai dangane da bayanan da ta samu, hukumar (HISBAH) ta Jihar Kano ta yi ram! Da kwamishinan ayyuka na musamman na Jihar Jigawa, Auwal Ɗalladi Sankara, a bisa zargin láląta da mátar aúré.
A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, mijin matar ne ya shigar da ƙara a gaban hukumar yana tuhumar kwamishinan da yin tarayya da matar tasa wanda hakan ya sanya hukumar yi masa ƙofar rago tare da kama shi.
Majiya daga Jaridar Daily Nigerian da Sahara Reporters sun tabbatar da cewa yanzu haka kwamishinan yana tsare a hedikwatar hukumar ta (HISBAH) da ke Kano tun daren jiya Alhamis bayan kama shin, wanda kuma bayan kammala bincike ne za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Me zaku ce?