Ƴan wasan Kano Pillars sun yi haɗari a hanyar Jos
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 19 na Kano Pillars ta yi haɗari.
Tawagar tayi haɗarin ne a hanyarsu ta zuwa filin wasa na Jos domin buga wasa a gasar matasa ta 'yan kasa da shekaru 19.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sashin yada labarai na kungiyar ya fitar a yau Talata.
"Muna bakincin sanar da cewa, motar da ke dauke da tawagar U-19 ta Kano Pillars FC ta yi hatsarin mota a yau, yayin da take kan hanyarta zuwa Sabon Filin Wasa na Jos don buga wasan cikon mako na 5 a gasar matasa ta U-19 da Plateau United .
"Wasu daga cikin 'yan wasan da direban sun ji rauni a wannan mummunan al'amari, kuma an gaggauta kai su asibiti don samun kulawar likitoci. Alhamdulillahi, ba a samu asarar rai ba a wannan lokaci, kuma tawagar likitocin na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki."
#Rana