Shugaban kasa Ya Kaddamar da Gidajen Alkalan Kotun Daukaka Kara a Abuja.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da sabbin gidaje guda 10 na alkalan Kotun Daukaka Kara a Katampe da ke Abuja, tare da jaddada kudurin gwamnatinsa na karfafa bangaren shari’a da tabbatar da ‘yancinsa.




Da yake jawabi ta bakin Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, shugaban kasar ya ce aikin wani muhimmin zuba jari ne da zai taimaka wajen inganta tsarin shari’a da dimokuradiyya.



Tinubu ya bayyana cewa samar da gidaje masu inganci da tsaro ga alkalai zai kara musu kwarin gwiwa tare da inganta gudanar da ayyukansu, yana mai cewa jin dadin ma’aikatan shari’a zuba jari ne ga ci gaban kasa.


Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi su kara zuba jari a bangaren shari’a, yana mai cewa nauyin tallafa wa kotuna ba na gwamnatin tarayya kadai ba ne.


A nasa bangaren, Nyesom Wike ya ce samar da irin wadannan ababen more rayuwa yana kara karfafa ‘yancin bangaren shari’a ne.


Ita kuwa Shugabar Kotun Daukaka Kara, Monica Dongban-Mensem, ta ce aikin zai samar wa alkalai ingantaccen muhalli da zai taimaka wajen bunkasa aikin shari’a.


An kaddamar da gidajen ne kwana guda bayan bude sabon ginin Kotun Daukaka Kara a Abuja, lamarin da ke nuna kokarin gwamnati na bunkasa bangaren shari’a a Najeriya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org